Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 25:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Da suka kama sarkin, sai suka kawo shi wurin Sarkin Babila a Ribla, inda aka yanke masa hukunci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Aka kama shi, aka kai shi gaban sarkin Babilon a Ribla, inda aka yanke masa hukunci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 25:6
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Fir'auna-neko ya sa shi a kurkuku a Ribla a ƙasar Hamat, don kada ya yi mulki a Urushalima. Ya kuma sa ƙasar ta riƙa ba da gandu, wato haraji, talanti ɗari na azurfa da talanti guda na zinariya.


Da aka kama Zadakiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babila a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babila ya yanke masa shari'a.


“Dukan matanka da 'ya'yanka za a kai su wurin Kaldiyawa, kai kanka kuma ba za ka tsere musu ba, amma Sarkin Babila zai kama ka, birnin kuma za a ƙone shi da wuta.”


Zadakiya Sarkin Yahuza kuwa, ba zai tsere wa Kaldiyawa ba, amma za a ba da shi a hannun Sarkin Babila. Zai yi magana da shi fuska da fuska, ya kuma gan shi ido da ido.


Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’


Saboda haka Ubangiji ya sa sarakunan yaƙi na Sarkin Assuriya su kamo Manassa da ƙugiyoyi, su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla, su kai shi Babila.


Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki suka kamo shi a filayen Yariko. Sojojinsa duka suka watse, suka bar shi.


Ba za ka tsere masa ba, amma lalle za a kama ka, a ba da kai a hannunsa. Za ka ga Sarkin Babila ido da ido, ka kuma yi magana da shi fuska da fuska. Za ka tafi Babila.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ