2 Sarakuna 25:23 - Littafi Mai Tsarki23 Sa'ad da shugabannin mayaƙa su da mayaƙansu suka ji Sarkin Babila ya naɗa Gedaliya ya zama hakimi, sai suka zo tare da mutanensu wurin Gedaliya a Mizfa, wato su Isma'ilu ɗan Netaniya, da Yohenan ɗan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, mutumin Netofa, da Yazaniya mutumin Ma'aka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202023 Sa’ad da dukan hafsoshin soja tare da mutanensu suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya a matsayin gwamna, sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa. Mutanen da suka zo su ne, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan ɗan Kareya, Serahiya ɗan Tanhumet mutumin Netofa, Ya’azaniya ɗan mutumin Ma’aka, tare da mutanensu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma Irmiya bai tafi ba, sai Nebuzaradan ya ce masa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan, wanda Sarkin Babila ya sa ya zama mai mulkin garuruwan Yahuza, ka zauna tare da shi da mutanen, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.” Sai ya ba Irmiya abinci da kyauta, sa'an nan ya sallame shi.