2 Sarakuna 24:8 - Littafi Mai Tsarki8 Yekoniya yana da shekara goma sha takwas sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Nehushta 'yar Elnatan, mutumin Urushalima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas da ya zama sarki, ya kuma yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Nehushta ’yar Elnatan, mutuniyar Urushalima. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.