Saboda haka Ubangiji ya ce Yehoyakim, Sarkin Yahuza, ba zai sami magāji wanda zai zauna a gadon sarautar Dawuda ba. Za a jefar da gawarsa a waje ta sha zafin rana, da dare kuma za ta sha matsanancin sanyi.
Sauran ayyukan Yehoyakim da irin abubuwan da ya yi na banƙyama, da irin laifofinsa, suna nan, an rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila da na Yahuza. Ɗansa Yekoniya kuwa ya gāji gadon sarautarsa.