Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 24:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ubangiji kuwa ya sa ƙungiyar maharar Kaldiyawa, da ta Suriyawa, da ta Mowabawa, da ta Ammonawa su yi gāba da Yahuza, su hallaka su bisa ga maganar Ubangiji, wadda ya faɗa wa bayinsa annabawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ubangiji ya aiki maharan Babiloniyawa, da na Arameyawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa. Ya aike su su hallaka Yahuda bisa ga maganar Ubangiji wadda ya furta ta bakin bayinsa annabawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 24:2
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma sa'ad da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kawo yaƙi a ƙasar, sai muka ce, ‘Bari mu tafi Urushalima domin muna jin tsoron sojojin Kaldiyawa da Suriyawa.’ Shi ya sa muke zaune a Urushalima.”


Ubangiji kuwa ya ce, “Zan kawar da jama'ar Yahuza daga gabana kamar yadda na kawar da jama'ar Isra'ila. Zan yi watsi da birnin nan da na zaɓa, wato Urushalima, da Haikalin da na ce sunana zai kasance a wurin.”


Sai al'ummai suka kafa masa tarko a kowane waje, Sun kafa masa tarko, Suka kama shi cikin wushefensu.


Saboda haka, ni Ubangiji, na ce zan ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa da hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, za su ci birnin.


zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.


‘Lokaci yana zuwa da za a kwashe duk abin da yake cikin gidanka, da abin da kakanninka suka tanada, zuwa Babila.


Sai ya shirya musu babbar liyafa. Sa'ad da suka ci suka sha, sai ya sallame su, suka koma wurin shugabansu. Suriyawa kuwa ba su ƙara kai wa ƙasar Isra'ila hari ba.


Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin kufai, Dutse inda Haikali yake zai zama kurmi.


Akwai wani mutum kuma wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji. Sunansa Uriya ɗan Shemaiya mutumin Kiriyat-yeyarim. Ya yi annabci gāba da birnin nan da ƙasan nan da magana irin ta Irmiya.


Saboda haka zan mai da wannan Haikali kamar Shilo, in mai da wannan birni ya zama abin la'ana ga dukan al'umman duniya.”


Suna zuwa daga manisantan ƙasashe, daga kan iyakokin duniya. Ubangiji yana zuwa da fushinsa, ya lalatar da dukan ƙasar.


“Ubangiji zai aukar maka da kwanakin wahala, kai da jama'arka, da dukan iyalin gidan sarauta, waɗanda suka fi muni tun lokacin da aka raba mulkin Isra'ila daga na Yahuza. Zai kawo Sarkin Assuriya!


Kafin yă gama magana, sai wani bara ya zo, ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa suka auka mana, suka kwashe raƙuma duka, suka kuma karkashe barorinka duka, sai ni kaɗai na tsira, na zo in faɗa maka.”


Saboda haka Ubangiji ya sa sarakunan yaƙi na Sarkin Assuriya su kamo Manassa da ƙugiyoyi, su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla, su kai shi Babila.


Za ta yi ta auko muku a kai a kai kowace safiya. Tilas ku sha ta dare da rana. Kowane sabon jawabin da zai zo muku daga wurin Allah, zai kawo muku sabuwar razana!


Ashe, abin gadon nan nawa ya zama dabbare-dabbaren tsuntsun nan ne mai cin nama? Tsuntsaye masu cin nama sun kewaye shi? Tafi, ka tattaro namomin jeji, Ka kawo su su ci.


A shekara ta huɗu ta mulkin Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi wa Irmiya magana a kan dukan mutanen Yahuza. A shekarar da Nebukadnezzar ya ci sarautar Babila,


Wannan shi ne yawan mutanen da Nebukadnezzar ya kai su bauta. A shekara ta bakwai ta sarautarsa, ya tafi da Yahudawa dubu uku da ashirin da uku (3,023).


Sihiyona tana miƙa hannuwanta, Amma ba wanda zai ta'azantar da ita. Gama Ubangiji ya umarci maƙwabtan Yakubu su zama maƙiyansa. Urushalima kuma ta zama ƙazantacciya a tsakaninsu.


Babilawa da dukan Kaldiyawa, da Fekod, da Showa, da Kowa, da dukan Assuriyawa tare da su, wato samari masu bansha'awa. Dukansu masu mulki ne, da shugabanni, da jarumawa, da shahararru, dukansu suna kan dawakai.


Ga shi, ina tā da Kaldiyawa, Al'umman nan mai zafi, mai fitina, Waɗanda suke tafiya ko'ina a duniya, Sun ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.


‘Ga shi, zan aukar da masifa a wurin nan, da a mazaunan wurin, bisa ga dukan maganar littafin nan wanda Sarkin Yahuza ya karanta,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ