2 Sarakuna 24:12 - Littafi Mai Tsarki12 Sai Yekoniya Sarkin Yahuza ya ba da kansa ga Sarkin Babila shi da tsohuwarsa, da fādawansa da hakimansa. Sarkin Babila ya kama shi yana da shekara takwas da sarautar, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Yehohiyacin sarkin Yahuda, da mahaifiyarsa, da masu yi masa hidima, da hakimansa, da kuma fadawansa duk suka miƙa kansu ga Nebukadnezzar. A shekara ta takwas ta mulkin sarkin Babilon, sarkin Babilon ya mai da Yehohiyacin ɗan kurkuku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kama Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, daga Urushalima, ya kai shi bautar talala a Babila, tare da sarakunan Yahuza, da gwanayen sana'a, da maƙera, dukansu, ya kawo su Babila. Sai Ubangiji ya nuna mini wannan wahayi. Na ga kwando biyu na ɓaure, an ajiye su a gaban Haikalin Ubangiji.