2 Sarakuna 23:3 - Littafi Mai Tsarki3 Sarki ya tsaya kusa da ginshiƙi ya yi alkawari ga Ubangiji, cewa zai bi Ubangiji da zuciya ɗaya, da dukan ransa. Zai kiyaye umarnansa, da farillansa, da dokokinsa, ya bi maganar alkawarin da aka rubuta a littafin. Dukan jama'a kuma suka yi alkawarin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, yă kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |