Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 23:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sa'an nan ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan jama'ar Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, da firistoci, da annabawa, da jama'a duka, ƙanana da manya. Sai ya karanta musu dukan maganar littafin alkawarin da aka iske a Haikalin Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sai ya haura zuwa cikin haikalin Ubangiji tare da mutanen Yahuda, da na Urushalima, da firistoci, da annabawa, dukan mutane, manya da ƙanana. Ya karanta musu duk kalmomin Littafin Alkawari, wanda aka samu a haikalin Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 23:2
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Hilkiya babban firist kuwa ya ce wa Shafan magatakarda, “Na iske littafin dokoki a cikin Haikalin Ubangiji.” Hilkiya kuwa ya ba Shafan littafin, shi kuwa ya karanta shi.


Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.


Da na sami taimakon Allah kuwa, ga ni a nan har yanzu, ina shaida wa babba da yaro, ba na faɗar kome sai abin da annabawa da Musa suka ce zai auku,


Zai sa wa dukan waɗanda suke tsoronsa albarka. Babba da yaro.


Kowa da kowa yana wurin, babba da ƙarami duk ɗaya ne, Bayi ma sun sami 'yanci.


Bayan da waɗannan kwanaki sun cika, sai sarki ya yi wa manya da ƙanana waɗanda suke a Shushan, wato masarauta, biki, har na kwana bakwai a filin lambun fādar sarki.


A wannan rana aka karanta daga littafin Musa a kunnuwan jama'a. A cikinsa aka tarar da inda aka rubuta, cewa kada Ba'ammone, ko mutumin Mowab ya shiga taron jama'ar Allah.


Sa'ad da suke tsaye a inda suke, sai suka ɗauki kashi ɗaya daga cikin huɗu na yini, suna karanta littafin dokokin Ubangiji Allahnsu. Suka kuma ɗauki kashi ɗaya daga cikin huɗu ɗin na yinin, suna ta hurta laifofi suna kuma yi wa Ubangiji Allahnsu sujada.


Suka koyar a Yahuza, suna tare da Littafin Shari'ar Ubangiji, wato Attaura. Suka shiga ko'ina a biranen Yahuza suka koyar da jama'a.


Duk wanda kuma bai nemi Ubangiji, Allah na Isra'ila ba, za a kashe shi, ko yaro ko babba, ko mace ko namiji.


Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da jama'ar Isra'ila sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar.


Suka kwashe mata da dukan waɗanda suke ciki manya da ƙanana, suka tafi da su. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe su, suka tafi.


Amma da suka kai shi can sai Ubangiji ya hukunta birnin, ya gigita su, ya yi musu azaba da marurai, yara da manya.


“Ku ɗauki littafin dokokin nan, ku ajiye shi tare da akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku domin ya zama shaida a kanku,


Sai suka bugi mutanen da suke ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu suna laluba inda ƙofa take.


Ubangiji kuma ya yi magana da Irmiya bayan da Zadakiya ya yi alkawari da dukan mutanen Urushalima don a yi musu shelar ba da 'yanci,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ