2 Sarakuna 23:19 - Littafi Mai Tsarki19 Dukan matsafai na kan tuddai da suke a garuruwan Samariya waɗanda sarakunan Isra'ila suka gina, har suka sa Ubangiji ya yi fushi, Yosiya ya watsar da su. Ya yi da su kamar yadda ya yi a Betel. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 Kamar yadda ya yi a Betel, Yosiya ya kawar da dukan ɗakunan gumaka a kan tuddan da sarakunan Isra’ila suka gina a garuruwan Samariya, waɗanda suka tozarta Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da aka gama duka, sai dukan Isra'ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al'amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa'an nan dukan jama'ar Isra'ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.