Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 23:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Ya kuma lalatar da matsafai na kan tuddan da suke gabashin Urushalima, kudu da Dutsen Hallaka, waɗanda Sulemanu Sarkin Isra'ila, ya gina wa Ashtoret gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh gunkin Mowab, da Milkom gunkin Ammonawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Sarkin kuma ya lalatar da masujadan kan tuddan da suke gabas da Urushalima, kudu da Tudun Hallaka, waɗanda Solomon sarkin Isra’ila ya gina don Ashtarot, ƙazantacciyar alliyar Sidoniyawa, da Kemosh ƙazantaccen allah na Mowab, da kuma Molek allahn banƙyama na mutanen Ammon.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 23:13
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sulemanu ya gina wa Kemosh, wato gunkin Mowab, da Molek, gunkin Ammonawa, masujadai a kan dutsen da yake gabas da Urushalima.


Gama Sulemanu ya bi Ashtoret ta Sidoniyawa, da Milkom, wato gunkin Ammonawa.


Kaitonku, ku mutanen Mowab! Ku masu sujada ga Kemosh kun lalace! Gumakanku sun sa mutane su zama 'yan gudun hijira, Mata kuwa, Sihon, Sarkin Amoriyawa ya kama su.


Da kuma waɗanda suke durƙusa wa rundunan sama a kan bene, Waɗanda sukan durƙusa, su rantse da Ubangiji, Duk da haka kuma sai su rantse da Milkom,


Masifar Mowab ta kusato, Halakarta kuma tana gaggabtowa.


Sa'an nan Kemosh zai kunyatar da Mowab, kamar yadda Betel wadda Isra'ilawa suka dogara gare ta ta kunyatar da su.


“Kun dogara ga ƙarfinku da wadatarku, Amma yanzu za a ci ku da yaƙi, Kemosh zai tafi bauta Tare da firistocinsa da shugabanninsa.


Na faɗa musu cewa, “Ba a kan irin wannan ba ne Sulemanu Sarkin Isra'ila ya yi laifi? A al'ummai, ba sarki kamarsa. Allahnsa ya ƙaunace shi, ya sarautar da shi a Isra'ila, duk da haka baren mata suka sa shi ya yi zunubi.


Domin Sulemanu ya rabu da ni, ya bauta wa Ashtoret, gunkiyar Sidoniyawa, da Kemosh, gunkin Mowab, da Milkom, gunkin Ammonawa. Bai yi tafiya a cikin tafarkuna ba, bai yi abin da yake daidai a gare ni ba, bai kiyaye dokokina, da ka'idodina kamar yadda Dawuda, tsohonsa, ya yi ba.


Sai suka yi wa Ubangiji kuka, suka ce, ‘Mun yi laifi domin mun bar bin Ubangiji, muka bauta wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot, amma yanzu muna roƙonka ka cece mu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.’


Isra'ilawa kuwa suka rabu da gumakan Ba'al da Ashtarot, suka bauta wa Ubangiji shi kaɗai.


Kai ba za ka mallaki abin da Kemosh, allahnka, ya ba ka mallaka ba? Dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya mallakar mana, za mu mallake shi.


Isra'ilawa suka sāke yi wa Ubangiji zunubi. Suka yi sujada ga Ba'al da Ashtarot, allolin Suriyawa, da na Sidon, da na Mowab, da na Ammonawa, da na Filistiyawa. Suka bar bin Ubangiji, suka daina yi masa sujada.


Suka bar yi wa Ubangiji sujada suka bauta wa gumakan nan, wato Ba'al da Ashtarot.


Masu ƙera gumaka ba su da ko tunanin da za su ce, “Na ƙone wani sashi na itacen nan. Na toya gurasa a garwashin, na kuma gasa nama, na ci shi, na kuwa ce sauran itacen zan sassaƙa gunki da shi. Ga ni yanzu, ina ta rusunawa gaban guntun itace!”


Gama yawan gumakansu sun kai yawan biranensu. Yawan bagadan da suke da su kuma sun kai yawan titunan Urushalima, abin kunya, bagadan ƙona wa Ba'al turare ne.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ