Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 23:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ya kawar da dawakan da sarakunan Yahuza suka keɓe wa rana, a ƙofar Haikalin Ubangiji, kusa da shirayin Natan-melek shugaban shirayin da yake cikin farfajiya. Haka kuma ya ƙone karusai waɗanda aka yi wa rana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Ya kawar da dawakan nan da sarakunan Yahuda suka keɓe wa gumakan nan na rana daga mashigin haikalin Ubangiji. Waɗannan dawakan suna kusa da ɗakin Natan Melek, ɗaya daga cikin dattawan sarki. Yosiya ya kuma ƙone kekunan yaƙi a yin sujada ga gumakan nan rana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 23:11
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya kuma kai ni farfajiya ta can cikin Haikalin Ubangiji. Na ga mutum wajen ashirin da biyar a ƙofar Haikalin Ubangiji a tsakanin shirayi da bagade, suka juya wa Haikalin Ubangiji baya, suka fuskanci wajen gabas, suna yi wa rana sujada.


Sai suka farfashe bagadai na Ba'al a gabansa, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu. Ya ragargaza Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da na zubi, ya maishe su ƙura. Ya barbaɗa su a kan kaburbura waɗanda suka miƙa hadayu a kansu.


Daga cikin dukan biranen Yahuza, ya kawar da masujadai da bagadan ƙona turare. A zamaninsa an sami zaman lafiya a mulkinsa.


Ya kuma tuɓe firistocin gumaka waɗanda sarakunan Yahuza suka naɗa domin su ƙona turare a matsafai na kan tuddai a garuruwan Yahuza, da kewayen Urushalima, da firistoci waɗanda suka ƙona turare ga Ba'al, da rana, da wata, da taurari, da dukan rundunan sama.


Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.


A ɗan ɗakin da take wajen yamma, akwai masu tsaro huɗu a hanyar, biyu kuma a ɗan ɗakin.


Idan ga hasken rana nake zuba ido, Ko ga hasken farin wata ne,


Sai ya kawo ni a fili na waje, ga ɗakuna da daɓe kewaye da filin. Akwai ɗakuna talatin a gaban daɓen.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ