Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 23:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Ya kuma lalatar da Tofet, wurin da yake kwarin 'ya'yan Hinnom, don kada kowa ya ƙara miƙa ɗansa ko 'yarsa hadaya ta ƙonawa ga Molek.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ya lalatar da Tofet, wanda yake a Kwarin Ben Hinnom, don kada kowa yă iya yin amfani da wurin don yă miƙa hadayar ɗansa, ko ’yarsa a wuta ga Molek.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 23:10
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.


Saboda haka rana tana zuwa da ba za a ƙara ce da wannan wuri Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a ce da shi Kwarin Kisa.


Kada ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa don a miƙa wa Molek, gama yin haka zai ƙasƙantar da sunan Allah. Shi Ubangiji ne.


Sun gina wa Ba'al masujadai a kwarin ɗan Hinnom don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga Molek, ni kuwa ban umarce su ba, ba shi kuwa a tunanina. Ga shi, sun aikata wannan abin banƙyama, don su sa Yahuza ta yi zunubi.”


Daga nan iyakar ta bi ta kwarin ɗan Hinnom a wajen kudancin kafaɗar Yebus, wato Urushalima. Ta kuwa bi ta dutsen da yake shimfiɗe daura da kwarin Hinnom wajen yamma, a arewacin ƙarshen kwarin Refayawa.


Kada a tarar da wani daga cikinku wanda zai sa 'yarsu ko ɗansu ya wuce ta tsakiyar wuta, ko mai duba, ko mai maita, ko mai bayyana gaibi, ko mai sihiri,


Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.


Sa'ad da kuke miƙa hadaya, kuna miƙa 'ya'yanku hadaya ta ƙonawa, kuna ƙazantar da kanku ta wurin gumakanku har wa yau, to, za ku iya tambayata, ya ku mutanen Isra'ila? Ni Ubangiji Allah ba na tambayuwa gare ku.


Na kuma bari su ƙazantar da kansu ta wurin hadayunsu, su kuma sa 'ya'yan farinsu su ratsa wuta. Na yi haka don in sa su zama abin ƙyama, don kuma su sani ni ne Ubangiji.


Kin karkashe 'ya'yana, kin sa su ratsa cikin wuta.


ku tafi kwarin ɗan Hinnom na mashigin Ƙofar Kasko, ka yi shelar maganar da zan faɗa maka a can.


Ya miƙa 'ya'yansa maza hadaya ta ƙonawa a kwarin ɗan Hinnom. Ya yi bokanci, ya yi duba, ya yi tsubbu, yana kuma sha'ani da makarai da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanar fushin Ubangiji.


Banda haka ma ya ƙona turare a kwarin ɗan Hinnom, ya ƙone 'ya'yansa maza bisa ga ƙazantattun al'adun al'ummai, waɗanda Ubangiji ya kore su daga gaban mutanen Isra'ila.


Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa ya kuma aikata sihiri, ya yi dūba. Ya yi ma'amala da masu mabiya da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.


Suka yi hadaya ta ƙonawa da 'ya'yansu mata da maza. Suka yi duba, suka yi sihiri, suka duƙufa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji, suka sa shi ya yi fushi.


Ya bi halin sarakunan Isra'ila. Har ma ya yi hadaya ta ƙonawa da ɗansa, kamar mugayen ayyukan al'ummai da Ubangiji ya kora a gaban mutanen Isra'ila.


Sulemanu ya gina wa Kemosh, wato gunkin Mowab, da Molek, gunkin Ammonawa, masujadai a kan dutsen da yake gabas da Urushalima.


Iyakar kuma ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskar kwarin ɗan Hinnon, wanda yake arewa wajen ƙarshen kwarin Refayawa. Ta kuma gangara zuwa kwarin Hinnom ta yi kudu daura da Yebusiyawa, ta gangara zuwa En-rogel.


ku da muguwar sha'awa take ƙonawa a tsakanin itatuwan oak, da ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa. Ku da kuka karkashe 'ya'yanku a cikin kwaruruka, da a ƙarƙashin duwatsu masu tsayi?


Ga shi, mutanen nan sun rabu da ni, sun ƙazantar da wannan wuri sun ƙona wa gumaka turare, waɗanda su, ko kakanninsu, ko sarakunan Yahuza, ba su san su ba. Sun cika wannan wuri da jinin marasa laifi.


da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da Azeka da ƙauyukanta. Haka suka yi zango daga Biyer-sheba zuwa kwarin Hinnom.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ