Sa'an nan ya haura zuwa Haikalin Ubangiji tare da dukan jama'ar Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, da firistoci, da annabawa, da jama'a duka, ƙanana da manya. Sai ya karanta musu dukan maganar littafin alkawarin da aka iske a Haikalin Ubangiji.
Joshuwa kuma ya tara dukan kabilan Isra'ila a Shekem, ya kuma kira dattawa, da shugabanni, da alƙalai, da jarumawan Isra'ila. Suka hallara a gaban Allah.