2 Sarakuna 22:4 - Littafi Mai Tsarki4 “Ka tafi wurin Hilkiya babban firist domin a lasafta yawan kuɗin da aka kawo cikin Haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tattara daga wurin jama'a. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 “Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.