Ku kyakkece zuciyarku, ba tufafinku kaɗai ba.” Ku komo wurin Ubangiji Allahnku. Gama shi mai alheri ne, mai jinƙai, Mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, Yakan tsai da hukunci.
da yake zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gabana sa'ad da ka ji yadda na yi magana gāba da wannan wuri, da kuma mazaunansa, cewa zai zama kufai da la'ana, kai kuwa ka keta tufafinka, ka yi kuka a gabana, hakika na ji kukanka.
Ubangiji ya ce, “Mutanen Yahuza sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun raina koyarwata sun ƙi bin umarnaina. Allolinsu na ƙarya waɗanda kakanninsu suka bauta wa, Sun sa su su ratse daga hanya.