2 Sarakuna 21:7 - Littafi Mai Tsarki7 Siffar gunkiyan nan Ashtoret wadda ya yi, ya kafa ta a Haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Sulemanu, “A cikin wannan Haikali a Urushalima wadda na zaɓa daga cikin dukan kabilan Isra'ila zan tabbatar da sunana har abada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel.