“Ka yi haƙuri da su shekaru da yawa, ka gargaɗe su, Annabawanka sun yi musu magana, amma sun toshe kunne. Saboda haka ka sa waɗansu al'ummai su mallaki jama'arka.
“Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka, Suka juya wa dokokinka baya, Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su, Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka. Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.
Amma mutanen Yahuza ba su kasa kunne ba. Manassa kuma ya yaudare su, suka aikata mugunta fiye da abin da al'umman da Ubangiji ya hallaka a gaban jama'ar Isra'ila suka aikata.
“Tun da yake Manassa, Sarkin Yahuza, ya aikata waɗannan abubuwa masu banƙyama, ya kuma aikata mugayen abubuwa fiye da dukan abin da Amoriyawa, waɗanda suka riga shi, suka aikata, ya kuma sa mutanen Yahuza su yi zunubi saboda gumakansa,
Amma Ubangiji ya faɗakar da jama'ar Isra'ila da jama'ar Yahuza ta bakin annabawa da kowane maigani, cewa su bar mugayen hanyoyinsu, su kiyaye umarnansa da dukan dokokinsa waɗanda ya umarci kakanninsu da su, waɗanda kuma ya aiko musu ta wurin bayinsa annabawa.