Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 20:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Hezekiya kuwa ya rasu. Sai ɗansa, Manassa, ya gāji gadon sarautarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Hezekiya ya huta tare da kakanninsa. Manasse ɗansa kuma ya gāje shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 20:21
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Hezekiya ya rasu, suka binne shi a sashe na bisa na hurumin 'ya'yan Dawuda, maza. Dukan Yahuza da mazaunan Urushalima suka girmama shi sa'ad da ya rasu. Sai Manassa ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.


Azariya ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a hurumin sarakuna, gama suka ce, “Shi kuturu ne.” Sai Yotam ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.


Manassa ya mutu, aka binne shi a lambun gidansa a gonar Uzza. Ɗansa Amon ya gāji gadon sarautarsa.


Manassa yana da shekara goma sha biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara hamsin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Hefziba.


Rehobowam kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce. Ɗansa, Abaija ya gāji sarautar.


Sulemanu ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda, wato Urushalima, ɗansa Rehobowam ya gaji sarautarsa.


Sa'an nan Dawuda ya rasu, aka binne shi a birnin Urushalima.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ