Amma in za ka yi addu'a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu'a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.
A waɗannan kwanaki sai Hezekiya ya yi rashin lafiya har yana gab da mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya zo wurinsa, ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka, gama mutuwa za ka yi, ba za ka warke ba.”
“Ka tuna da ni yanzu, ya Ubangiji, ina roƙonka, da yadda na yi tafiya a gabanka da aminci, da zuciya ɗaya, na aikata abin da yake mai kyau a gabanka.” Sai ya yi ta rusa kuka.