Domin haka, sai ka kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce. Saboda ka ce mini in daina yin annabci gāba da jama'ar Isra'ila, kada kuwa in yi wa zuriyar Ishaku ɓaɓatu,
Ya Urushalima sarakunanki da jama'arki sun zama kamar Saduma da Gwamrata. Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa muku. Ku mai da hankali ga abin da Allahnmu yake koya muku.
Amma Elisha ya ce, “Kasa kunne ga abin da Ubangiji ya ce! Gobe war haka za a sayar da mudu na lallausan gari a bakin shekel guda, da mudu biyu na sha'ir a bakin shekel guda a ƙofar garin Samariya.”
Makaiya kuwa ya ce, “Ka ji maganar Ubangiji, gama na ga Ubangiji yana zaune a kursiyinsa. Dukan taron mala'ikun Sama suna tsaye a wajen damansa da na hagunsa.