Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 20:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Sai annabi Ishaya ya tafi wurin sarki Hezekiya ya ce masa, “Daga ina ne waɗannan mutane? Me suka ce maka?” Hezekiya ya amsa, ya ce, “Sun zo daga ƙasa mai nisa, wato Babila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Sai annabi Ishaya ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya tambaye shi ya ce, “Me mutanen nan suka ce, kuma daga ina suka fito?” Sai Hezekiya ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Daga Babilon.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 20:14
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suna zuwa daga manisantan ƙasashe, daga kan iyakokin duniya. Ubangiji yana zuwa da fushinsa, ya lalatar da dukan ƙasar.


Faɗakarwar da mutumin da ya gogu da al'amuran duniya ya yi ga wanda yake da niyya ya kasa kunne, tamaninta ya fi na zoben zinariya, ko kayan ado da aka yi da zinariya tsantsa.


Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri, Zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai, Domin kullayaumi ina addu'a gāba da mugayen ayyuka.


Suka amsa masa suka ce, “Daga ƙasa mai nisa ƙwarai, bayinka suka zo saboda sunan Ubangiji Allahnka, gama mun ji labarinsa da dukan abin da ya yi a Masar,


Suka tafi wurin Joshuwa da Isra'ilawa a zango a can Gilgal, suka ce musu, “Daga ƙasa mai nisa muka fito, yanzu fa, sai ku yi alkawari da mu.”


Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba,


Hezekiya kuwa ya marabce su, ya kuma nuna musu dukan taskokin dukiyarsa na azurfa, da na zinariya, da na turare, da na mai mai daraja, da na makaman yaƙinsa, da dukan abin da yake akwai a cikin ɗakunan ajiyarsa. Ba abin da ya rage daga cikin gidansa, ko a mulkinsa wanda bai nuna musu ba.


Ishaya ya ce, “Me suka gani a fādarka?” Hezekiya ya ce, “Sun ga duk abin da yake ciki, ba wani abu kuma daga cikin taskokina da ban nuna musu ba.”


Babilawa da dukan Kaldiyawa, da Fekod, da Showa, da Kowa, da dukan Assuriyawa tare da su, wato samari masu bansha'awa. Dukansu masu mulki ne, da shugabanni, da jarumawa, da shahararru, dukansu suna kan dawakai.


Allah kuwa ya zo wurin Bal'amu ya ce masa, “Suwane ne mutanen da suke tare da kai?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ