Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 2:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni zuwa Kogin Urdun.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi tare.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan, Ubangiji ya aike ni Urdun.” Sai Elisha ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka ci gaba da tafiya tare.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 2:6
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni har zuwa Betel.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi Betel.


Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari cewa, ‘Sa'ad da kuka shiga gefen ruwan Urdun, sai ku tsaya cik a wurin.’ ”


Amma Dawuda ya rantse masa, ya ce, “Mahaifinka ya hakikance na sami tagomashi a wurinka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada ya baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji da kai kuma, mataki ɗaya yake tsakanina da mutuwa!”


Ibrahim ya ɗauki itacen hadayar ƙonawa, ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuma ya ɗauki wuta da wuƙa a hannunsa. Dukansu biyu kuwa suka tafi tare.


Ibrahim ya ce, “Allah zai tanada wa kansa ragon hadayar ƙonawa, ya ɗana.” Sai su biyu suka tafi tare.


Amma Rut ta ce, “Kada ki yi ta roƙona in rabu da ke, ko in bar binki, gama inda za ki tafi, ni ma can zan tafi, inda kuma za ki zauna, ni ma can zan zauna. Mutanenki za su zama mutanena, Allahnki kuma zai zama Allahna.


Sa'an nan Hannatu ta ce, “Gafara dai, ba ka tuna da ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana roƙon Ubangiji.


Sai macen ta ce, “Na rantse da Ubangiji da kai kuma, ba zan bar ka ba.” Sai Elisha ya tashi, ya bi ta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ