Sai ta kama hanya, ta tafi wurin annabi Elisha a Dutsen Karmel. Sa'ad da annabi Elisha ya gan ta zuwa, sai ya ce wa Gehazi, wato baransa, “Duba, ga Bashunemiya can.
Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin Ubangiji ne a nan, wanda zai tambayar mana Ubangiji?” Sai ɗaya daga cikin fādawan Sarkin Isra'ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, na'ibin Iliya.”
Sa'an nan sarki ya aiki shugaba tare da mutum hamsin su taho da Iliya. Mutumin kuwa ya haura wurin Iliya a kan dutse, ya ce masa, “Ya mutumin Allah, sarki ya umarta ka sauko.”