Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 2:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni har zuwa Betel.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi Betel.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka dakata a nan; Ubangiji ya aike ni Betel.” Amma Elisha ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka gangara zuwa Betel.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 2:2
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Ina roƙonka, ka dakata a nan, gama Ubangiji ya aike ni zuwa Kogin Urdun.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka tafi tare.


Sai macen ta ce, “Na rantse da Ubangiji da kai kuma, ba zan bar ka ba.” Sai Elisha ya tashi, ya bi ta.


Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Elisha, ina roƙonka ka dakata a nan gama Ubangiji ya aike ni Yariko.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Sai suka tafi Yariko.


Sa'an nan Hannatu ta ce, “Gafara dai, ba ka tuna da ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana roƙon Ubangiji.


Idan kun yi rantsuwa kuka ce, ‘Har da ran Ubangiji kuwa,’ Da gaskiya, da aminci, da adalci, Sa'an nan sauran al'umma za su so in sa musu albarka, Za su kuma yabe ni.”


Ya tafi gaban bagaden da ya gina a Betel a rana ta goma sha biyar ga wata na takwas, wato watan da ya zaɓa don kansa. Ya kafa wa jama'ar Isra'ila idi. Sai ya tafi don ya ƙona turare a kan bagaden.


Yanzu, ya maigida, na rantse da ran Ubangiji da kuma ranka, ka ga Ubangiji ya hana ka zubar da jini, da ɗaukar wa kanka fansa, sai ka bar maƙiyanka da waɗanda suke nema su cuce ka su zama kamar Nabal.


Ya kira sunan wurin nan Betel, amma da farko, sunan birnin, Luz.


Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki.


Ya kafa siffar maraƙi ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan.


Sa'ad da Saul ya ga Dawuda ya tafi ya yi yaƙi da Goliyat, ya ce wa Abner, sarkin yaƙinsa, “Abner, ɗan wane ne wannan saurayi?” Abner ya amsa, ya ce, “Ranka ya daɗe, ya sarki, ban sani ba.”


Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata 'yan maruƙa biyu da zinariya. Sa'an nan ya ce wa jama'arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra'ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.”


Daga nan Elisha ya haura zuwa Betel. A hanya sai ga waɗansu samari sun fito daga cikin gari, suna yi masa eho, suna cewa, “Ka bar wurin nan, kai mai saiƙo.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ