Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 19:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Da sarki Hezekiya ya ji wannan magana, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa rigar makoki, sa'an nan ya shiga Haikalin Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Da sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya shiga haikalin Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 19:1
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka zo wurin Hezekiya da tufafinsu ketattu, suka faɗa masa irin maganar da Rabshake ya yi.


Da Ahab ya ji wannan magana, sai ya yage tufafinsa, ya sa na makoki, ya yi azumi, ya kwanta a tsummokin makoki, ya tashi yana tafiya a hankali.


Sai Yakubu ya kyakkece rigunansa, ya yi ɗamara da majayi, ya yi kukan ɗansa har kwanaki masu yawa.


“Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, suna sanye da tsumma, suna hurwa da toka.


Sai dukan mutane da dabbobi su sa tufafin makoki. Kowa ya roƙi Allah da gaske, kowa kuma ya bar mugayen ayyukan da yake yi.


Duk da haka da sarkin da barorinsa suka ji maganar, ba wanda ya ji tsoro, balle su keta rigunansu don baƙin ciki.


Amma sa'ad da suke ciwo, nakan sa tufafin makoki, Na ƙi cin abinci, Na yi addu'a da kaina a sunkuye,


Sa'ad da na ji wannan, sai na yayyage rigata da alkyabbata, na tsittsiga gashin kaina da na gemuna, na zauna a ruɗe.


Da sarki ya ji maganar macen, sai ya keta tufafinsa, sa'ad da yake wucewa ta kan garun birni. Sai mutane suka gani, ashe, yana saye da rigar makoki a ciki.


Da Sarkin Isra'ila ya karanta takardar, sai ya keta tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne, da zan kashe in rayar, har mutumin nan zai aiko mini da cewa in warkar da mutum daga kuturtarsa? Ku duba fa, ku ga yadda yake nemana da faɗa.”


“Ka ga yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana? Da yake ya ƙasƙantar da kansa a gabana, ba zan kawo masifar a zamaninsa ba, sai a zamanin ɗansa ne, zan kawo masifar a kan gidansa.”


Wani mutumin kabilar Biliyaminu ya gudu daga dāgar yaƙin ya zo Shilo da tufafinsa ketattu ga kuma ƙura a kansa.


Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi!


Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.”


Sa'an nan sai Sarkin Assuriya, wato Sennakerib, ya janye ya koma Nineba.


Sai mutanen Nineba suka gaskata Allah, suka tsai da shawara, cewa kowa da kowa ya yi azumi. Dukan mutane kuwa babba da yaro, suka sa tufafin makoki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ