2 Sarakuna 18:5 - Littafi Mai Tsarki5 Hezekiya ya dogara ga Ubangiji Allah na Isra'ila. Ba a sami kamarsa a cikin dukan sarakunan Yahuza ba, waɗanda suka yi sarauta a gabansa, ko waɗanda suka yi bayansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Hezekiya ya dogara ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. Ba a yi wani kamar sa ba cikin dukan sarakunan Yahuda; ko kafin shi, ko kuma bayansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”