Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 18:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ya kawar da wuraren tsafi na kan tuddai, ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffar Ashtoret. Ya kuma farfashe macijin tagulla wanda Musa ya yi, gama har zuwa lokacin jama'ar Isra'ila suna miƙa masa hadaya ta turaren ƙonawa. Aka ba macijin suna Nehushatan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Ya kawar da masujadan kan tudu, ya farfasa keɓaɓɓun duwatsu, ya sassare ginshiƙan Ashera. Ya fashe macijin tagullan da Musa ya yi, gama har zuwa lokacin nan Isra’ilawa suna ƙona turare gare shi. (An ba shi suna Nehushtan.)

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 18:4
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da aka gama duka, sai dukan Isra'ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al'amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa'an nan dukan jama'ar Isra'ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.


“Amma idan ka ce mini, ‘Ina dogara ga Ubangiji Allahnmu,’ to, ba masujadansa na kan tuddai da bagadansa ne Hezekiya ya rurrushe ba? Yana ce wa mutanen Yahuza da Urushalima, ‘Za ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima?’


Duk da haka ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba, mutane suka ci gaba da miƙa hadayu da ƙona turare a kan tuddan.


Ya bi halin tsohonsa, Asa, bai karkace ba. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Duk da haka ba a rushe wuraren tsafin na tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu, suka ƙona turare a tuddan.


Da mutanen garin suka tashi da safe, sai ga bagaden Ba'al a farfashe, gumakan kuma da suke kusa da shi, an sare. Bijimi na biyu kuma, an miƙa shi hadaya a kan bagaden da aka gina.


A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimin mahaifinka, da wani bijimin bana bakwai. Sa'an nan ka rushe bagaden gunkin nan Ba'al na mahaifinka, ka sare gumakan da suke kusa da shi.


Ga yadda za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza al'amudansu, ku sassare ginshiƙansu na tsafi, ku ƙaƙƙone sassaƙaƙƙun siffofinsu.


Zan lalatar da masujadanku, in rurrushe bagaden ƙona turarenku, in jefar da gawawwakinku a kan gumakanku, raina kuwa zai ji ƙyamarku.


Ba za ku rusuna wa allolinsu ba, balle fa ku bauta musu, kada ku yi yadda suke yi. Sai ku hallaka allolinsu ɗungum, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu.


Suka sa shi ya yi fushi saboda Masujadansu na arnanci. Suka sa ya ji kishi saboda gumakansu.


Gama ya sāke giggina masujadai waɗanda Hezekiya, tsohonsa, ya rurrushe. Ya kakkafa bagadai don Ba'al, ya kuma yi Ashtarot. Ya yi sujada ga dukan rundunar sama, ya bauta musu.


Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da gumakan Ashtarot daga ƙasar, ka sa zuciyarka ga neman Allah.”


Sarki Ahaz ya umarci Uriya firist cewa, “Sai ka miƙa hadaya ta ƙonawa ta safe, da hadaya ta gari ta maraice, da hadaya ta ƙonawa ta sarki, da hadayarsa ta gari, da hadaya ta ƙonawa ta dukan jama'ar ƙasar, da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, ka yayyafa dukan jinin hadaya ta ƙonawa, da dukan jinin hadayu a bisa babban bagaden. Amma bagaden tagulla zai zama nawa don yin ibada.”


Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba, amma mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a matsafai na kan tuddai. Shi ne ya gina ƙofa ta bisa ta Haikalin Ubangiji.


Duk da haka ba a kawar da wuraren tsafi na kan tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu da ƙona turare a wuraren tsafi na kan tuddai.


Amma ba a kawar da wuraren yin tsafi a tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadaya, da ƙona turare a matsafai na kan tuddai.


Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel.


Sai ku rurrushe bagadansu, ku farfashe al'amudansu, ku sassare gumakansu.


Gama ya gina matsafai a kan tuddai waɗanda Hezekiya tsohonsa ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba'al bagadai, ya kuma yi gunkiyan nan, wato Ashtoret, kamar yadda Ahab, Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya yi wa taurari sujada, ya bauta musu.


Ya ci gaba ya ce, “Ko za ka ce mini kana dogara ga Ubangiji Allahnka? Shi ne wannan da Hezekiya ya lalatar masa da wuraren sujada da bagadai, sa'an nan ya faɗa wa jama'ar Yahuza da na Urushalima su yi sujada ga bagade ɗaya kurum.


Ni ne na tsaya a tsakanin Ubangiji da ku a lokacin don in faɗa muku maganar Ubangiji, gama kun ji tsoro saboda wutar, ba ku kuma hau dutsen ba. “Ubangiji ya ce,


Suka fitar da gumakan da suke cikin haikalin Ba'al, suka ƙone su.


Sai dukan jama'ar ƙasa suka tafi haikalin Ba'al suka farfashe shi, da bagadensa da siffofinsa. Suka kuma kashe Mattan firist na Ba'al a gaban bagaden. Yehoyada kuwa ya sa matsara su yi tsaron Haikalin Ubangiji,


Ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffofin gumakan, sa'an nan ya rufe wurarensu da ƙasusuwan mutane.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ