Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 18:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Amma Rabshake ya ce musu, “Ai, ubangidana bai aike ni in yi wannan magana ga ubangidanku da ku kaɗai ba, amma ga dukan mutanen da suke zaune a kan garu, waɗanda aka ƙaddara su tare da ku don su ci najasarsu su sha fitsarinsu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Amma shugaban sojojin ya ce, “Ai, ba gare ku da sarkinku kaɗai ne shugabana ya aike ni ba. Amma har ga mutanen da suke zaune a kan katangar birnin, waɗanda za su ci kashinsu, su sha fitsarinsu!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 18:27
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan ya ce mini, “To, zan bar ka ka mori taroson shanu maimakon najasa, don ka dafa abincinka.”


Ubangiji ya ce, “Haka jama'ar Isra'ila za su ci ƙazantaccen abincinsu a cikin sauran al'umma inda za a kai su bautar talala.”


Su waɗanda suka ci abubuwa masu daɗi, Sun halaka a titi. Su waɗanda aka goye su da alharini, Yanzu suna kwance a kan tsibin toka.


Sukan yi wa waɗansu ba'a, Suna faɗar mugayen abubuwa, Masu girmankai ne su, suna shawara A kan yadda za su zalunci waɗansu.


Aka yi yunwa mai tsanani a Samariya a lokacin da aka kewaye ta da yaƙin, har aka riƙa sayar da kan jaki a bakin shekel tamanin, an kuma sayar da rubu'in mudu na kashin kurciya a bakin shekel biyar.


Sai Sarkin Assuriya ya aiki Tartan, da Rabsaris, da Rabshake, tare da sojoji da yawa daga Lakish zuwa ga sarki Hezekiya a Urushalima. Suka haura zuwa Urushalima, suka tsaya kusa da wuriyar ruwan kududdufi wanda yake kan tudu, wanda yake a kan karauka zuwa wurin wanki.


Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa, suka ce wa Rabshake, “Muna roƙonka, ka yi magana da mu barorinka da harshen Aramiya gama muna jinsa, kada ka yi magana da mu da harshen Yahudanci, har mutanen da suke kan garu su ji.”


Sa'an nan Rabshake ya tsaya, ya yi kira da ƙarfi da harshen Yahudanci, ya ce, “Ku ji maganar mai girma, Sarkin Assuriya!


Ya amsa ya ce, “Kuna tsammani babban sarki ya aiko ni don in daɗa wa ku da sarki kurum dukan magana? Sam, ina magana ne da jama'ar da suke a kan garu, waɗanda za su ci kāshinsu su kuma sha fitsarinsu, kamar yadda ku kanku za ku yi.”


Harshen jinjiri ya liƙe a dasashinsa saboda ƙishi, 'Yan yara suna roƙon abinci, Amma ba wanda ya ba su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ