2 Sarakuna 17:6 - Littafi Mai Tsarki6 A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, sarkin Assuriya ya ci Samariya da yaƙi ya kuma kwashe Isra’ilawa zuwa Assuriya. Ya tsugunar da su a Hala, da a Gozan a bakin Kogin Habor da kuma a garuruwan Medes. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.