Mutumin Habasha zai iya sāke launin fatar jikinsa? Ko kuwa damisa za ta iya sāke dabbare-dabbarenta? Idan haka ne, ku kuma za ku iya yin nagarta, Ku da kuka saba da yin mugunta.
Har wa yau suna yin yadda suka yi a dā. Ba su yi tsoron Ubangiji ba, ba su bi dokoki, ko ka'idodi, ko shari'a, ko umarnan Ubangiji ba, waɗanda ya umarci 'ya'yan Yakubu, wanda ya sa wa suna Isra'ila.
Waɗannan al'ummai suka yi wa Ubangiji sujada, amma suka kuma yi ta bauta wa gumakansu. Haka kuma 'ya'yansu da jikokinsu suka yi kamar yadda kakanninsu suka yi. Haka suke yi har wa yau.