Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 17:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Sa'an nan Sarkin Assuriya ya umarta a aiki firist ɗaya daga cikin firistocin da aka kwashe daga can, ya tafi, ya zauna can domin ya koya musu shari'ar Allahn ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Sai sarkin Assuriya ya ba da umarni cewa, “A sami wani daga cikin firistocin da aka kwaso zuwa bauta daga Samariya, yă koma yă zauna a can, yă koya wa mutanen abin da allahn ƙasar yake bukata.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 17:27
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Yerobowam ya naɗa firistoci don masujadansa, saboda siffofin bunsurai, da na maruƙa, waɗanda ya yi.


Bisa ga umarnin Ubangiji, sai annabin ya ta da murya, ya ce, “Ya bagade, bagade, Ubangiji ya ce za a haifi ɗa a gidan Dawuda, sunansa Yosiya wanda zai miƙa firistoci na masujadan tuddai hadaya a kanka, wato firistoci waɗanda suke ƙona turare. Za a ƙone ƙasusuwan mutane a bisa kanka.”


Ya kuma gina masujadai a tuddai, sa'an nan ya sa waɗansu daga cikin mutane waɗanda ba Lawiyawa ba, su zama firistoci.


Sa'an nan Mika ya ce, “Yanzu na sani Ubangiji zai sa mini albarka, da yake na sami Balawe ya zamar mini firist.”


Sai aka faɗa wa Sarkin Assuriya cewa, “Al'umman da ka kwashe ka zaunar da su a garuruwan Samariya ba su san shari'ar Allahn ƙasar ba, domin haka ya aiki zakoki a cikinsu, suna ta karkashe su.”


Sai firist ɗaya daga cikin firistocin da suka kwashe daga Samariya, ya zo, ya zauna a Betel. Shi kuwa ya koya musu yadda za su yi tsoron Ubangiji.


“Kai kuma, Ezra, bisa ga hikimar da Allahnka ya ba ka, sai ka naɗa mahukunta da alƙalai waɗanda za su yi wa mutanen da suke a lardin Yammacin Kogi shari'a, wato dukan waɗanda suka san shari'a. Waɗanda ba su san shari'a ba kuwa, sai ka koya musu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ