2 Sarakuna 17:23 - Littafi Mai Tsarki23 har lokacin da Ubangiji ya kawar da su daga gabansa kamar yadda ya faɗa ta bakin bayinsa, annabawa. Saboda haka aka fitar da jama'ar Isra'ila daga ƙasarsu zuwa Assuriya har wa yau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202023 har Ubangiji ya kawar da su daga gabansa, kamar yadda ya gargaɗe su ta bakin bayinsa annabawa. Saboda haka aka kwashi mutanen Isra’ila daga ƙasarsu zuwa bauta a Assuriya, har wa yau kuwa suna can. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.