Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 17:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Saboda wannan Ubangiji ya husata da jama'ar Isra'ila, ya kawar da su daga gabansa, ba wanda aka rage, sai dai kabilar Yahuza.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi ƙwarai da Isra’ila, ya kuma kawar da su daga gabansa. Kabilar Yahuda kaɗai aka bari,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 17:18
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma Sulemanu, zai sami kabila ɗaya saboda bawana Dawuda, da kuma ɗaya saboda Urushalima, wato birnin da na zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka.


Duk da haka ba zan ƙwace mulkin duka ba, amma zan ba ɗanka kabila guda, saboda bawana Dawuda, saboda kuma Urushalima wadda na zaɓa.”


Ubangiji ya ce, “Ifraimu ta kewaye ni da ƙarairayi, Jama'ar Isra'ila kuwa ta kewaye ni da munafuncinta, Yahuza kuma ta tayar wa Allah, Wato tana gāba da Mai Tsarki, mai aminci.


Da dukan mutane suka ji, cewa Yerobowam ya komo, sai suka aika a kirawo shi ga taron jama'a. Suka naɗa shi Sarkin Isra'ila duka. Ba wanda ya bi gidan Dawuda, sai dai kabilar Yahuza.


Duk da haka zan ba ɗansa kabila guda, domin bawana Dawuda ya kasance da fitila kullum a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa sunana.


Ba za su zauna a ƙasar Ubangiji ba, Amma mutanen Ifraimu za su koma Masar. Za su ci haramtaccen abinci a Assuriya.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da a ce Musa da Sama'ila za su tsaya a gabana, duk da haka zuciyata ba za ta komo wurin mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana su yi tafiyarsu!


Ubangiji kuwa ya ce, “Zan kawar da jama'ar Yahuza daga gabana kamar yadda na kawar da jama'ar Isra'ila. Zan yi watsi da birnin nan da na zaɓa, wato Urushalima, da Haikalin da na ce sunana zai kasance a wurin.”


Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, bai ba su baya ba saboda alkawarinsa da Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Bai yarda ya hallaka su ba, bai kuma yi watsi da su ba har wa yau.


Amma kamar yadda Ubangiji Allahnku ya cika alkawaran da ya yi muku, haka nan kuma Ubangiji zai aukar muku da masifu, har ya hallaka ku daga ƙasan nan mai albarka da Ubangiji Allahnku ya ba ku.


to, sai ku tabbata Ubangiji Allahnku ba zai dinga korar al'umman nan daga gabanku ba, za su zama muku azargiya, da tarko, da bulala a kwiyaɓunku, da ƙayayuwa a idanunku. Da haka za ku ƙare sarai daga cikin kyakkyawar ƙasan nan da Ubangiji Allahnku ya ba ku.


“Idan jama'arka sun yi maka zunubi, gama ba mutumin da ba ya yin zunubi, har ka yi fushi da su, ka kuwa bashe su a hannun abokan gāba, har suka kwashe su zuwa bauta a wata ƙasa mai nisa,


A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.


Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata, Zan ga yadda ƙarshensu zai zama. Gama su muguwar tsara ce, 'Ya'ya ne marasa aminci.


Danawa fa suka kafa gunkin domin su yi masa sujada. Jonatan, ɗan Gershom, ɗan Musa, shi da 'ya'yansa maza, suka zama firistocin Danawa, har zuwa ranar da aka kwashe mutanen zuwa bauta.


Zan jefar da ragowar gādona, in bashe su a hannun abokan gāba, za su zama ganima da abin waso ga dukan abokan gābansu,


Hakika haka ya faru ga Yahuza bisa ga umarnin Ubangiji domin a kawar da su daga gaban Ubangiji saboda dukan zunubin Manassa da ya aikata,


Sa'an nan zan koya wa masu zunubi umarnanka, Za su kuwa komo wurinka.


Zan kore ku daga gabana kamar yadda na yi wa dukan 'yan'uwanku, dukan zuriyar Ifraimu.’ ”


Al'amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra'ila da Yahuza, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala. Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.


A cikin mahaifa kakansu Yakubu ya kama diddigen ɗan'uwansa, Sa'ad da ya zama baligi ya yi kokawa da Allah.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ