Ubangiji ya ce, “Kada ku yi wa kanku gumaka, ko ku kafa sassaƙaƙƙiyar siffa, ko al'amudi. Kada kuma ku kafa wata siffa ta dutse a ƙasarku da za ku durƙusa mata, gama ni ne Ubangiji Allahnku.
Suka ƙona turare a kan wuraren tsafi na kan tuddai kamar yadda al'ummar da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka aikata mugayen abubuwa, suka su Ubangiji ya yi fushi.
domin kada ku yi cuɗanya da sauran al'umman da take zaune tare da ku, kada ku ambaci sunayen gumakansu, ko ku rantse da su, ko ku bauta musu, ko ku sunkuya musu.
Gama sa'ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su, sa'ad da suka ga kowane tudu da kowane itace mai ganye, sai suka miƙa hadayunsu a wuraren nan suka tsokane ni da hadayunsu. A wuraren ne suka miƙa hadayunsu na turare mai ƙanshi da hadayu na sha.’