2 Sarakuna 16:14 - Littafi Mai Tsarki14 Sai ya kawar da bagaden tagulla wanda aka keɓe ga Ubangiji, ya sa shi arewacin sabon bagadensa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Sai ya cire bagaden tagulla wanda aka keɓe ga Ubangiji, ya sa shi a gaban haikalin wato, tsakanin ƙofar shiga haikalin Ubangiji da sabon bagaden. Ya ajiye shi a gefen arewa na sabon bagaden. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sarki Ahaz ya umarci Uriya firist cewa, “Sai ka miƙa hadaya ta ƙonawa ta safe, da hadaya ta gari ta maraice, da hadaya ta ƙonawa ta sarki, da hadayarsa ta gari, da hadaya ta ƙonawa ta dukan jama'ar ƙasar, da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, ka yayyafa dukan jinin hadaya ta ƙonawa, da dukan jinin hadayu a bisa babban bagaden. Amma bagaden tagulla zai zama nawa don yin ibada.”