22 Menahem ya mutu, ɗansa Fekahiya ya gaji sarautarsa.
22 Menahem ya huta tare da kakanninsa. Fekahiya ɗansa kuma ya gāje shi.
Sauran ayyukan Menahem, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
A shekara ta hamsin ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Fekahiya ɗan Menahem, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara biyu.
Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla masa maƙarƙashiya, ya buge shi a Ibleyam, ya kashe shi, sa'an nan ya hau gadon sarautarsa.