2 Sarakuna 15:19 - Littafi Mai Tsarki19 Tiglatfilesar, mai mulkin Assuriya, ya kawo wa ƙasar yaƙi, Menahem kuwa ya ba Tiglat-filesar talanti dubu (1,000) na azurfa, don dai ya taimake shi yadda sarautarsa za ta kahu sosai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 Sai Ful sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar hari, Menahem kuwa ya ba shi talenti dubu na azurfa don yă sami goyon bayansa, yă kuma ƙarfafa kahuwa mulkin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Yowash Sarkin Yahuza ya kwashe dukan kyautai na yardar rai waɗanda Yehoshafat, da Yoram, da Ahaziya, kakanninsa, sarakunan Yahuza suka keɓe, ya kuma kwashe kyauta ta yardar rai ta kansa, da dukan zinariya da aka samu a baitulmalin Haikalin Ubangiji da baitulmalin gidan sarki, ya aika wa Hazayel, Sarkin Suriya. Sa'an nan Hazayel ya tashi ya bar Urushalima.
“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.