Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 15:16 - Littafi Mai Tsarki

16 A lokacin nan sai Menahem ya hallaka Tifsa da dukan waɗanda suke cikinta, da karkararta tun daga Tirza, domin ba su karɓe shi ba, saboda haka ya hallaka ta, ya tsattsage dukan matan da suke da juna biyu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 A lokacin nan sai Menahem ya taso daga Tirza, ya kai wa Tifsa hari da kowa wanda yake a birnin da kewayenta, don sun ƙi su buɗe ƙofofinsu. Ya kori Tifsa daga aiki, ya kuma tsattsaga cikin dukan mata masu juna biyu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 15:16
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?” Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”


Samariya za ta ɗauki hakkin zunubinta, Gama ta tayar wa Allahnta. Za a kashe mutanenta da takobi. Za a fyaɗa jariranta a ƙasa, A kuma tsage matanta masu ciki.”


Sulemanu ya mallaki dukan ƙasar da yake yamma da Kogin Yufiretis, daga Tifsa har zuwa birnin Gaza. Ya mallaki dukan sarakuna yammacin Yufiretis. Akwai zaman lafiya ko'ina a mulkinsa da ƙasashen maƙwabta.


Ubangiji ya ce, “Mutanen Ammon sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don haɗamarsu ta ƙasa, Suka tsaga mata masu ciki a Gileyad.


Sauran ayyukan Shallum duk da makircin da ya ƙulla, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.


Abimelek kuwa ya zo ya yaƙi hasumiyar. Ya je kusa da ƙofar hasumiyar don ya ƙone ta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ