Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 14:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Aka ƙulla makirci a kansa a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma aka aika zuwa Lakish, aka kashe shi a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Suka ƙulla masa maƙarƙashiya a Urushalima, ya gudu zuwa Lakish, amma suka aika har Lakish aka kashe shi a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 14:19
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Joshuwa kuma ya zarce daga Libna, da shi da Isra'ilawa duka, zuwa Lakish, suka kewaye ta da yaƙi, suka auka mata.


Ku mutanen Lakish, ku ɗaura wa dawakai karusai, Gama ku kuka fara yin zunubi a Sihiyona, Gama an iske laifofin Isra'ila cikinku.


Fādawansa kuwa suka ƙulla masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa.


Sai Sarkin Assuriya ya aiki Tartan, da Rabsaris, da Rabshake, tare da sojoji da yawa daga Lakish zuwa ga sarki Hezekiya a Urushalima. Suka haura zuwa Urushalima, suka tsaya kusa da wuriyar ruwan kududdufi wanda yake kan tudu, wanda yake a kan karauka zuwa wurin wanki.


Sai Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya aika zuwa wurin Sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka ƙyale ni, duk abin da ka ɗora mini zan ɗauka.” Sai Sarkin Assuriya ya ce wa Hezekiya Sarkin Yahuza ya ba shi talanti ɗari uku na azurfa, da talanti talatin na zinariya.


Hosheya ɗan Ila kuwa ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya, ya buge shi ya kashe shi, sa'an nan ya ci sarauta a shekara ta ashirin ta sarautar Yotam ɗan Azariya.


Sai shugaban sojojinsa, wato Feka, ɗan Remaliya daga Gileyad, tare da mutum hamsin suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kashe Fekahiya tare da Argob da Ariye a Samariya a fādarsa. Da suka kashe shi, sai Feka ya zama sarki.


Menahem ɗan Gadi daga Tirza ya zo Samariya ya bugi Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya hau gadon sarautarsa.


Shallum ɗan Yabesh ya ƙulla masa maƙarƙashiya, ya buge shi a Ibleyam, ya kashe shi, sa'an nan ya hau gadon sarautarsa.


Adonizedek Sarkin Urushalima, ya aika zuwa ga Hoham Sarkin Hebron, da Firam Sarkin Yarmut, da Yafiya Sarkin Lakish, da Debir Sarkin Eglon, ya ce,


Sauran ayyukan da Amaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.


Aka kawo gawar a kan dawakai, aka binne a Urushalima a makabartar kakanninsa a birnin Dawuda.


sa'ad da sojojin Sarkin Babila suke yaƙi da Urushalima da kuma dukan biranen da suka ragu na Yahuza, wato Lakish da Azeka. Waɗannan su kaɗai ne biranen Yahuza masu garu da suka ragu.


Da Ahaziya Sarkin Yahuza, ya ga haka, sai ya gudu ta hanyar Bet-haggan.Yehu kuwa ya bi shi, ya ce, “Shi ma a harbe shi.” Sai suka harbe shi a cikin karusarsa a hawan Gur, wanda yake kusa da Ibleyam. Sai ya gudu zuwa Magiddo, ya mutu a can.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ