12 Mutanen Isra'ila suka ci na Yahuza. Sai kowane mutum ya gudu gida.
12 Isra’ila suka fatattaki Yahuda, kowa kuwa ya tsere zuwa gidansa.
Suka ɗauki gawar Absalom, suka jefa ta cikin wani rami mai zurfi a kurmin, suka tula tsibin duwatsu a kanta. Dukan Isra'ilawa kowa ya tsere zuwa gidansa.
Filistiyawa kuwa suka yi yaƙi gadan-gadan, suka ci mutanen Isra'ila. Mutanen Isra'ila suka gudu, kowa ya nufi gidansa. Aka kashe Isra'ilawa da yawa, wato mutum dubu talatin (30,000).
A wajen faɗuwar rana aka yi wa sojoji shela aka ce, “Kowa ya koma garinsu da ƙasarsu.”