Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 13:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Rundunar Yehowahaz kuwa ba ta fi mahaya hamsin, da karusai goma, da dakarai dubu goma (10,000) ba, gama Sarkin Suriya ya hallaka rundunar, ya yi kaca kaca da ita kamar ƙura a masussuka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ba abin da ya rage na rundunar Yehoyahaz sai mahayan dawakai hamsin, kekunan yaƙi goma da kuma sojoji ƙasa dubu goma. Gama sarkin Aram ya hallaka sauran, ya kuma yi kaca-kaca da su kamar ƙura a masussuka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 13:7
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce, “Mutanen Dimashƙu sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun zalunci mutanen Gileyad da zalunci mai tsanani.


A kwanakin an Ubangiji ya soma rage ƙasar Isra'ila. Hazayel kuwa ya yaƙe su a karkarar Isra'ila,


Dubun dubbai suna cikin kwarin da za a yanke shari'a! Gama ranar Ubangiji ta kusa zuwa a kwarin yanke shari'a.


“Wane ne wannan da ya kawo mai yin nasara daga gabas, Ya kuma sa ya ci nasara a dukan inda ya tafi? Wa ya ba shi nasara a kan sarakuna da al'ummai? Takobinsa ya sassare su sun zama kamar ƙura! Kibansa sun warwatsar da su kamar ƙaiƙayi a gaban iska!


Zan yi ciniki da kai da sunan babban sarki, wato Sennakerib. Zan ba ka dawakai dubu biyu idan za ka iya samun yawan mutanen da za su hau su!


Zan murƙushe su har su zama ƙura Wadda iska take kwashewa, Zan tattake su kamar caɓi a titi.


Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?” Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”


Aka tara mutanen Isra'ila, aka ba su guzuri, suka tafi, su yi yaƙi da Suriyawa. Isra'ilawa suka kafa sansani a gabansu kamar 'yan garkuna biyu na awaki, amma Suriyawa suka cika ƙasar.


Sai ya tara sojoji matasa na hakiman larduna, mutum ɗari biyu da talatin da biyu. Sa'an nan kuma, ya tara dukan mutanen Isra'ila dubu bakwai (7,000).


Sama'ila ya tashi daga Gilgal zuwa Gibeya ta Biliyaminu. Da Saul ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, ya tarar wajen mutum ɗari shida ne.


Na murƙushe su, sun yi laushi kamar ƙura, Na tattake su kamar caɓi a kan tituna, na kuwa watsar da su.


Sauran ayyukan Yehowahaz da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.


“Na aukar muku da annoba irin wadda na aukar wa Masar. Na karkashe samarinku a wurin yaƙi, Na kwashe dawakanku. Na cika hancinku da ɗoyin sansaninku. Duk da haka ba ku komo wurina ba.


Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ