Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 13:10 - Littafi Mai Tsarki

10 A shekara ta talatin da bakwai ta sarautar Yowash Sarkin Yahuza, Yehowash ɗan Yehowahaz ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi shekara goma sha shida yana sarauta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 A shekaru talatin da bakwai ta Yowash sarkin Yahuda, Yehowash ɗan Yehoyahaz ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki shekaru goma sha shida.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 13:10
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yehowahaz kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowash ɗansa ya gāji sarautarsa.


Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai rabu da dukan zunubin Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa jama'ar Isra'ila su yi zunubi. Ya bi halin Yerobowam ɗan Nebat.


A shekara ta biyu ta sarautar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila, Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza ya ci sarauta.


Ubangiji kuwa ya ce wa Yehu, “Da yake ka yi abin da yake daidai a gare ni, ka yi wa gidan ahab bisa ga dukan abin da yake a zuciyata, 'ya'yanka, har tsara ta huɗu, za su ci sarautar Isra'ila.”


A shekara ta bakwai ta sarautar Yehu, Yowash ya ci sarautar. Ya yi shekara arba'in yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Zibiya ta Biyer-sheba.


A shekara ta ashirin da uku ta sarautar Yowash ɗan Ahaziya Sarkin Yahuza, Yehowahaz ɗan Yehu ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha bakwai.


Amaziya ɗan Yowash Sarkin Yahuza, ya yi shekara goma sha biyar bayan rasuwar Yehowash ɗan Yehowahaz Sarkin Isra'ila.


Wannan shi ne alkawarin da Ubangiji ya yi wa Yehu, cewa 'ya'yansa maza za su zauna a gadon sarautar Isra'ila har tsara ta huɗu. Haka kuwa ya zama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ