2 Sarakuna 12:9 - Littafi Mai Tsarki9 Sa'an nan Yehoyada, firist, ya ɗauki akwati, ya huda rami a murfin, sa'an nan ya ajiye shi kusa da bagade a sashin dama na shiga Haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka saka dukan kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Yehohiyada firist ya ɗauki akwatin ya huda rami a murfinsa. Ya ajiye shi kusa da bagade a hannun dama na haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka zuba dukan kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji a cikin akwatin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel.