2 Sarakuna 12:4 - Littafi Mai Tsarki4 Yowash ya ce wa firistoci, “Dukan kuɗin tsarkakan abubuwa da ake kawowa a Haikalin ubangiji, da kuɗin da aka tsara wa kowane mutum, da kuɗin da aka bayar da yardar rai, da ake kawowa a Haikali, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Yowash ya ce wa firistoci, “Ku tattara dukan kuɗin da ake kawo a matsayin hadayu masu tsarki na haikalin Ubangiji, kuɗin da aka tattara a ƙidaya, kuɗin da aka tattara daga wa’adin da mutum ya yi, da kuma kuɗin da aka kawo na yardan rai a haikali. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Yowash Sarkin Yahuza ya kwashe dukan kyautai na yardar rai waɗanda Yehoshafat, da Yoram, da Ahaziya, kakanninsa, sarakunan Yahuza suka keɓe, ya kuma kwashe kyauta ta yardar rai ta kansa, da dukan zinariya da aka samu a baitulmalin Haikalin Ubangiji da baitulmalin gidan sarki, ya aika wa Hazayel, Sarkin Suriya. Sa'an nan Hazayel ya tashi ya bar Urushalima.