Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 12:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Gat har ya cinye ta, ya kuma shirya zai yi yaƙi da Urushalima.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 A wannan lokaci, Hazayel sarkin Aram ya haura, ya kai wa Gat hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Sa’an nan ya juya don yă yaƙi Urushalima.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 12:17
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma Samariyawa suka ƙi karɓarsa, domin niyyarsa duk a kan Urushalima take.


Da lokacin karɓarsa a Sama ya gabato, ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima.


To, sai ku ji maganar Ubangiji, ya ku sauran mutanen Yahuza, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Idan zuwa Masar kuka sa gaba don ku tafi ku zauna a can,


Bayan haka kuma Dawuda ya ci Filistiyawa da yaƙi, ya mallake su, ya ƙwace Gat da garuruwanta daga hannunsu.


Beriya, da Shimai, su ne shugabannin gidajen kakanninsu da suke zaune a Ayalon waɗanda suka kori mazaunan Gat,


Duk wanda zai tsere wa Hazayel, Yehu zai kashe shi. Wanda kuma ya tsere wa Yehu. Elisha zai kashe shi.


Dawuda ya tashi tare da mutum ɗari shida da suke tare da shi zuwa wurin Akish, ɗan Mawok, Sarkin Gat.


Sa'an nan Asa ya kwashe dukan azurfa da zinariya da suka ragu a ɗakunan ajiya na Haikalin Ubangiji, da na gidan sarki, ya ba barorinsa su kai wa Ben-hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, ya ce,


A kwanakin an Ubangiji ya soma rage ƙasar Isra'ila. Hazayel kuwa ya yaƙe su a karkarar Isra'ila,


tun daga Urdun har zuwa wajen gabas, da dukan ƙasar Gileyad, da ta Gad, da ta Ra'ubainu, da ta Manassa, tun daga Arower wadda dake kusa da kwarin Arnon haɗe da Gileyad da Bashan.


Ubangiji kuwa ya husata da jama'ar Isra'ila, sai ya dinga ba da su a hannun Hazayel Sarkin Suriya, da hannun Ben-hadad ɗan Hazayel.


Ahaz kuma ya kwashe azurfa da zinariya da suke cikin Haikalin Ubangiji, da wadda take cikin baitulmalin sarki, ya aika wa mai mulkin Assuriya kyauta.


Zai yunƙuro da dukan ƙarfin mulkinsa, zai zo ya gabatar da shawarar salama, ya aikata ta. Zai aurar masa da 'yarsa don ta lalatar da mulkin abokin gabansa, amma wannan dabara ba za ta ci ba.


“Sun zo don su yi kama-karya. Ana jin tsoronsu tun ma kafin su zo. Sun tattara bayi kamar yashi.


Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ka'idar yinsu iri ɗaya ce. Firist wanda ya yi kafarar, zai ɗauki abin da ya ragu.


Kowace hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, da duk wadda aka yi a tukunya ko a kaskon tuya, za su zama na firist wanda ya miƙa hadaya.


Abin da ya ragu daga cikin hadaya mafi tsarki da ake miƙa mini zai zama rabonka da na 'ya'yanka, wato daga kowace hadaya, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ