2 Sarakuna 12:10 - Littafi Mai Tsarki10 Sa'ad da suka gani akwai kuɗi da yawa a cikin akwatin, sai magatakardan sarki, da babban firist suka zo, suka ƙirga kuɗin da yake a Haikalin Ubangiji suka ƙunsa shi a babbar jaka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Duk sa’ad da suka ga kuɗin sun ƙaru a akwatin, sai marubucin fada da babban firist, su ƙirga kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji su sa a jakankuna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Duk lokacin da Lawiyawa suka kawo wa 'yan majalisar sarki babban akwatin sa'ad da suka gan shi cike da kuɗi, sai magatakardan sarki, da na'ibin babban firist, su zo su juye kuɗin da suke cikin babban akwatin, sa'an nan su mayar da shi a inda yake. Haka suka yi ta yi kullum, har suka tara kuɗi masu yawan gaske.
Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel.