2 Sarakuna 11:14 - Littafi Mai Tsarki14 Da ta duba, sai ta ga sarki a tsaye kusa da ginshiƙi bisa ga al'ada, shugabanni da masu busa kuwa suna tsaye kusa da sarki. Dukan mutanen ƙasar suna ta murna suna ta busa ƙaho. Sai Ataliya ta kece tufafinta, ta yi ihu, tana cewa, “Tawaye, tawaye!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗanda kuma suke kusa da su har zuwa Issaka, da Zabaluna da Naftali, sun kawo abinci a kan jakuna, da raƙuma, da alfadarai, da takarkarai. Suka kawo abinci mai yawa, wato gāri da kauɗar ɓaure da nonnan busassun 'ya'yan inabi, da ruwan inabi, da man zaitun. Suka kuma kawo shanu da tumaki domin yanka a ci. Duk an yi wannan domin a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra'ila.