2 Sarakuna 10:7 - Littafi Mai Tsarki7 Da wasiƙar ta iso wurinsu, sai suka kwashi 'ya'yan sarki guda saba'in, suka karkashe su. Suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezreyel. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan ’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan Yehu ya rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “Idan kuna goyon bayana, idan kuma kun shirya za ku yi mini biyayya, to, sai ku fille kawunan 'ya'yan Ahab, sa'an nan ku zo wurina a Yezreyel gobe war haka.” 'Ya'yan sarki, maza, su saba'in ne, suna a hannun manyan mutanen birni ne waɗanda suke lura da su.