Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 10:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sa'an nan Yehu ya rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “Idan kuna goyon bayana, idan kuma kun shirya za ku yi mini biyayya, to, sai ku fille kawunan 'ya'yan Ahab, sa'an nan ku zo wurina a Yezreyel gobe war haka.” 'Ya'yan sarki, maza, su saba'in ne, suna a hannun manyan mutanen birni ne waɗanda suke lura da su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Sai Yehu ya sāke rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “In a gefena kuke, to, sai ku yi biyayya da ni, ku fille kawunan ’ya’yan maigidanku, ku kawo mini a Yezireyel war haka gobe.” To, ’ya’yan sarki, su saba’in, suna tare da manyan birni waɗanda suke lura da su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 10:6
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma Yesu ya ce masa, “Kada ku hana shi. Ai, duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”


Wanda ba nawa ba ne, gāba yake da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.


“Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa. A'a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi. Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.


Sai ya ɗaga idanunsa wajen tagar, ya ce, “Wa yake wajena?” Sai babani biyu ko uku suka dube shi,


Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta 'ya'ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni.


Ya ce wa Musa, “Ɗauki sugabannin jama'a, ka rataye su a rana a gabana don in huce daga fushin da nake yi da Isra'ilawa.”


Sai wakilin gidan, da wakilin birnin, da dattawa, da masu lura da 'ya'yan sarki, suka aika wurin Yehu suka ce, “Mu barorinka ne, duk abin da ka umarce mu, za mu yi. Ba za mu naɗa wani sarki ba, sai ka yi duk abin da ka ga ya yi maka kyau.”


Da wasiƙar ta iso wurinsu, sai suka kwashi 'ya'yan sarki guda saba'in, suka karkashe su. Suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezreyel.


Da safe, sa'ad da ya fita, ya tsaya, sai ya ce wa mutane duka, “Ba ku da laifi, ni ne na tayar wa maigidana har na kashe shi, amma wane ne ya kashe dukan waɗannan?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ