2 Sarakuna 10:5 - Littafi Mai Tsarki5 Sai wakilin gidan, da wakilin birnin, da dattawa, da masu lura da 'ya'yan sarki, suka aika wurin Yehu suka ce, “Mu barorinka ne, duk abin da ka umarce mu, za mu yi. Ba za mu naɗa wani sarki ba, sai ka yi duk abin da ka ga ya yi maka kyau.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Saboda haka sarkin fada, da gwamnan birnin, da dattawa, da kuma masu lura da ’ya’yan suka aika da saƙo ga Yehu, cewa, “Mu bayinka ne, za mu kuma yi duk abin da ka ce. Ba za mu naɗa kowa sarki ba; sai ka yi abin da ka ga ya fi kyau.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan Yehu ya rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “Idan kuna goyon bayana, idan kuma kun shirya za ku yi mini biyayya, to, sai ku fille kawunan 'ya'yan Ahab, sa'an nan ku zo wurina a Yezreyel gobe war haka.” 'Ya'yan sarki, maza, su saba'in ne, suna a hannun manyan mutanen birni ne waɗanda suke lura da su.